Fitaccen mawakin hausa Hausa Hip Hop Shu’aibu Ahmad Abbas Lilin Baba ya angwance da matarsa fitacciyar jarumar Kannywood Ummi Rahab.
A yau ranar asabar 18 ga watan yuni aka daura auren nasu a jihar Kano, kuma sun kasance suna soyayya wadda har ta kai su ga aure.
Ummi Rahab ta kasance daya daga cikin matasan taurarin mata a masana’antar Kannywood, kuma tun tana yarinya take shirin fim din hausa.

https://www.instagram.com/reel/Ce8C6yeIsxI/?igshid=MDJmNzVkMjY=