fbpx
Tuesday, September 29
Shadow

Hotuna: Daga Taimako an saka masa guba a abinci, ya mutu aka kwace mai Mota

Wannan shine Mallam Garba Direba Mai dauko mota daga Cotonou Jamhuriyar Benin zuwa Nijeriya.

 

Ya dauki fasinja daga Gaya zuwa Dosso a Kasar Nijer, kafin su je Dosso lokacin shan ruwa ya yi wato buda baki, sai fasinjan ya shawarce shi da su karasa wani kauye a nan kan hanyar su ta zuwa Dosso don yin buda baki, a nan dai fasinjan ya ce da shi nan kauyensu ne, ya shiga gida ya kawo musu abinci suka ci.

 

 

Bayan barin su garin kafin su isa Dosso, Mallam Garba ya fara jin barci yana raba hanya, ashe wannan abinci da suka ci akwai guba a ciki, a takaice fasinjan ya karbi mota ya kuma ajiye Mallam Garba a daji yana ta amai har Allah Ya karbi ransa, shi kuma ya yi awun gaba da motar kiran highlander 2005 model.

 

 

Rayuwar duniya ta canza, za ka jawo mutum jikinka da niyyar ka taimake shi, amma da zarar ya samu dama sai ya cutar da kai saboda cin amana, shi ya sa yanzu idan za ka taimaki mutum taimake shi daga nesa, amma kar ka kuskura ka jawo wanda baka san tarihin sa ba jikinka.

 

 

Muna rokon Allah Ya tonawa barawon nan asiri, shi kuma Malam Garba Allah Ka yafe masa, Ka sa mutuwa hutu ce a gare shi, Ka bawa iyalan shi hakurin jure wannan bakin ciki da damuwa.

Daga Datti Assalafiy.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *