fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Hotuna: Dan Kwallon Najeriya, Ahmed Musa da Gwamnan Jihar Filato na buga Kwallon Golf

Tauraron dan kwallon Najeriya, Ahmed Musa kenan a wadannan hotunan inda yake tare da Gwamnan jihar Filato Simon Lalong sike buga kwallon Golf.

 

Ya saka hotunan ne a shafinsa na sada zumunta inda yai fatan cewa in Allah ya yarda kwanannan wannan cuta zata wuce.

Ahmed Musa na bugawa kungiyar Alnassr ta kasar Saudiyya wasa saidai sanadiyyar cutar Coronavirus/COVID-19 data sa aka dakatar da wasannin kwallon kafa a Duniya baki daya, ya dawo gida Najeriya tare da Iyalansa.

 

A baya dai an watsa labarin karya dake cewa Ahmed Musa ya kamu da cutar Coronavirus/COVID-19,  labarin da yafito da kansa ya karyata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.