An samu fashewar wata tankar mai a kan gadar Otedola, kusa da Berger a jihar Legas ranar Asabar.
An ce fashewar ta auku ne da misalin karfe 3 na dare, Ya zuwa lokacin wannan rahoton, babu wani cikakken bayanin abin da ya faru ko adadin wadanda suka jikkata.
