fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Hotuna: Gwamna Yahya Bello ya kaiwa shugaba Buhari fom din takarar shugaban kasa da ya siya

Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello ya kaiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari fom din takarar shugaban kasa da ya siya.

 

Gwamna Bello shine dan takarar APC na farko da ya fitar da Miliyan 100 ya sayi fom din takarar shugaban kasar da ake ta cece-kuce cewa yayi tsada.

Gwamna Bello na daga cikin ‘yan takarar dake ganin cewa, kada a yi mulkin karba-karba a shekarar 2023, a bar kowane dan takara ya nemi kujerar shugaban kasar me rabo ka dauka.

 

Saidai da yawa na ganin da wuya Gwamnan na jihar Kogi, Yahya Bello ya kai Labari, lura da yanda jama’ar jiharsa ke kuka  musamman kan rashin biyan albashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.