Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya baiwa wani Almajiri dan jiharsa kyautar Naira Miliyan 5.
Gwamnan ya masa kyautar ne saboda Taraktar noma da ya kirkiro dan karfafa masa gwiwa.


Matashin dan shekaru 25, Laminu Mohammed da ya fito daga karamar hukumar Gubio ta jihar bai taba karatun Boko ba.
Makarantar Allo ce ya yi kuma wannan hikima tasa daga Allah ne.