Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya ziyarci garuruwan Ngoshe, Warabe da Pulka na karamar hukumar Gwoza da ke jihar, inda ya raba kayan abinci ciki har da N24million ga ‘yan kasa masu rauni a yankin.
A cewar wata sanarwa da aka wallafa a kan kafafen sada zumunta na gwamnan, Gwamna Zulum ya sanya ido a wajen rabon kayan abinci da tsabar kudi N24m a tsabar kudi ga mutane 1,200 masu rauni a garin Ngoshe da suka dawo daga Pulka da Maiduguri.


Kowane magidanci ya samu buhun masara mai nauyin kilogiram 50, buhun 1 na sorghum 50kg, buhun wake 25kg, buhun shinkafa kilo 12.5, lita 5 na man girki, sauran kayan hadin da kuma kudi na N20,000,” in ji sanarwar.