fbpx
Monday, August 8
Shadow

Hotuna: Gwamnan Zamfara ya siyawa kwamishinoninsa Motocin Alfarma na Miliyan Dari 5 da 70

Gwamnan jihar Zamfara,Bello Matawalle ya rabawa kwamishinoninsa da wasu manyan mutane a jihar Motoci kirar Camry 2020 wanda ake sayar dasu akan akalla Naira Miliyan 30 kowacce.

 

Hakan ya bayyanane daga bakin wasu da suka amfana da kyautar Motocin inda suka rika daka hotunan Motocin suna godiya ga gwamnan a shafukan sada zumunta.

Wani ma’abocin shafin Twitter ya bayyana cewa an rabawa kwamishinonin 19 a jihar Motocin wanda jimullar kudinsu ya kai Naira Miliyan 570.

Wasu sun yaba da wannan Kyauta inda wasu kuma suka rika Allah wadai da hakan ganin cewa Jihar Zamafara na daya daga cikin jihohin da suka fi fama da Talauci a Najeriya.

A wannan hali da ake ciki na matsin cutar Coronavirus/COVID-19 gwamnatoci na kokarin ganin sun samarwa mutanensu saukin Rayuwa ta hanyar basu tallafin kayan Abinci dana kudi.

Karanta wannan  A rika sanar dani daga yau domin ba zan laminci kashe mutane a kudu maso gabashin Najeriy ba, cewar shugaba Buhari

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=280039706489645&id=100034508523657

A jiyane dai aka samu mutum na farko daya kamu da cutar Coronavirus/COVID-19 a jihar ta Zamfara.

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=1017600365325846&id=100012276752012

A baya an zargi ‘yan Majalisun Tarayya da siyawa kansu irin wadannan motocin Alfarma inda lamarin ya jawo musu suka, saidai daga baya sun fito sun karyata lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

5 Comments

 • Aliyu moriki

  Allah ya shirya shugabanin mu muna fama da rashi da yan zaman banza da yinwa a zamfara akke takashe muna kudi ta hanyar da batadace ba wallahi kuji tsoron Allah akwai mutuwa kuma akwai kwanci kabari

 • Ibrahim Aliyu Ahmad

  Hmm rayuwa kenan munanan muna fama da abinda zamuci dakyar amm anje ana barnata wa talakawa kudi t Inda bai dace ba, Allah kazamo gatanmu bijahi Sayyidi Rasulillah s,a,w

 • Sagir Abdullahi

  Nayi iya nazarina aduniya akan tsarin shugabanci. Amma wallahi babu wata kasa aduniya da take da mahaukata shugabanni kamar Nigeria..
  Shugabanni Nigeria 98% wallahi mahaukane.Babu tunani ko hankali adukkan lamuransu na rayuwa.kuma basa tsoran Allah.basa tuna hisabin daza,ayi agaban Allah Rayuwa sukeyi kamar dabbobi wani lokacin har gara dabbobi dasu.

 • Ibrahim yahaya

  A wani lokaci daya wuce kasar sin wato China ta taba cewa mulkin dimukwaradiya bedace da Africa ba Kuma saboda me sukace haka saboda Africa rayuwa akeyi makar rayuwar namun daji wanda duk yafi karfin wani zai maida abincinshi

Leave a Reply

Your email address will not be published.