fbpx
Friday, February 26
Shadow

Hotuna: Gwamnatin jihar Legas ta rusa wasu gine-gine a Banana Island saboda saba dokokin gini

Hukumar kula da tsarin gine-gine a jihar Legas, ta rusa wasu gine-gine a Island Banana saboda rashin bin ka’idoji da dokokin gini na jihar.

Kwamishinan tsare-tsaren da raya birane, Dokta Idris Salako, wanda shine ya jagorancin ruguza gine-ginen, yace rusa wajen ya zama dole saboda anyi ginin ba bisa ka’ida ba.

Ya kara da cewa mutane da dama suna yin gine-gine ba tare da bin doka ko neman shawarar hukumar ba, shiyasa suka dauki wannan matakin domin ya zama misali ga yan baya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *