Gwamnatin jihar Legas ta fara raba kayayyakin abinci ga mazauna jihar da aka hanawa fita domin gudun bazuwar cutar Coronavirus.
Wakilin BBC a Legas y ace tun kafin dokar hana fita a biranen Legas da Abuja da Ogun ta fara aiki ne, gwamnatin ta Legas ta fara raba kayan abincin
The Special Adviser, Office of Civic Engagement, Princess Aderemi Adebowale, leading the distribution of Stimulus Food Package at Epe Local Government, Ikosi Ejirin and Eredo LCDAs@jidesanwoolu @drobafemihamzat @IruVI_Sole#LASG #ForAGreaterLagos #LagosAgainstCovid19 pic.twitter.com/yAI2ACkYi2
— The Lagos State Govt (@followlasg) March 31, 2020
Sai dai kuma ta ce akwai wasu daga cikin al’ummar jihar da ke fargabar cewa tallafin ba zai iso gare su ba inda wasunsu suka bukaci a sa ido sosai don gudun kada wasu su karkatar da tallafin.