fbpx
Tuesday, September 29
Shadow

Hotuna: Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin ciyar da ‘yan makaranta abinci a gida a jihar Legas

Gwamnatin tarayya ta kaddanar da shirin ciyar da yara ‘yan makaranta Abinci a gida a jihar Legas.

 

Ministar walwala da kula da Ibtila’i,  Sadiya Umar Farouk ce ta kaddamar da shirin inda ta bayyana cewa tsarine da aka yi bisa umarnin shugaban kasa,Muhammadu Buhari.

Daraktar kula da ‘yan gudun hijira ta ma’aikatar, Mrs. Margaret Ukegbu ce ta wakilci Ministar inda ta bayyana cewa shirin zai shafi mutane 37, 589 wanda suka hada da iyayen yaran da yaran da masu basu kulawa.

 

Ta kara da cewa kowane gida zai samu Kilogram 5 na shinkafa, sai Kilogiram 5 na gero, man girki, Gishi, tumaturi, da kuma kwai guda 15.

Tace kwarru wajan fannin samar da abincin gina jikine suka bada shawarar bayar da wannan kalar abinci dan kuwa yana da matukar amfani wajan gina jiki.

 

Ta kara da cewa an zabi jihar Legas ta zama daya daga cikin wanda za’a kaddamar da aikin a cikintane saboda yanda yake gaba-gaba wajan yaki da cutar Coronavirus/COVID-19.

Ta kuma godewa gwamna Sonwo Olu bisa taimakon daya bayar wajan ganin wannan aiki ya tabbata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *