Tauraron mawakin Hausa, Ali Isa Jita ya fito takarar neman zama Gwamnan Kano.
Fastocin yakin neman zabensa sun rika yawo a shafukan sada zumunta inda abokan aikinsa irin su Nazir Ahmad Sarkin Waka, Ado Gwanja da Sauransu suka rika yada hotunan a shafukansu na sada zumunta.
Shi dai Jita bai saka fastar a shafinsa ba amma ga dukkan alamu, Abokan aikinsa sun yi na’am da wannan yunkurin.
