fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Hotuna: Kalli Sahun Takun kafa, Takubba da Tasar, Annabi Muhammad(SAW)

Ita dai daular Usmaniyya ta kafu ne a shekara ta 1299, 27 ga watan Yuli, sannan ta ruguje a 29 ga watan Octoba shekara ta 1923, wato ta kwashe tsawon shekara 600 kenan tana gudana.

Wanda ya fara kafa ta kuwa shine Uthman na farko, wanda ake kiransa Attagul.

Mallam Aminu Ibrahim Daurawa wanda fitaccen malamin addinin musulunci ne a Najeriya ya shaidawa BBC cewa abubuwan da ake jinginawa Manzon Allah waɗanda aka same su a ƙasar Turkiyya ya faru ne a lokacin Sarki Abdulhamid II, a shekarar 1914.

Wani sarki a lokacin yaƙin duniya ya so ya kai farmaki Madina domin ya yi ta’addanci, don haka wannan sarki yasa aka tara sojoji masu yawa aka tura su domin su je su tsare Madina, su kuma kwaso duk wani abu dake da alaƙa da Manzon Allah don kada a maimaita ƙona alkyabbar Manzon Allah da Magul suka yi a Bagadaza.

Sahun takun Annabi Muhammad kenan da aka nuna a wani gidan adana kayan tarihin musulmai dake birnin Santambul na Turkiyya a ranar 16 ga Nuwamban 2017. Gidan adana kayan tarihi na birnin Santambul dake unguwar Sultanahmet na ƙunshe da kayayyakin tarihi na Turkawa da na Musulunci. Sannan akwai tarin kayan kere-kere, na gilashi, da duwatsu da kayan kwalliya, da kayan karafa na yumɓu, da kuma manyan katifu na Turai, waɗanda kayan tarihi ne da ba safai ake samunsu daga bangarorin duniyar Musulunci ba.
Bayanan hoto,Sahun takun Annabi Muhammad kenan da aka nuna a wani gidan adana kayan tarihin musulmai dake birnin Santambul na Turkiyya a ranar 16 ga Nuwamban 2017. gidan dake unguwar Sultanahmet na ƙunshe da kayayyakin tarihi na Turkawa da na Musulunci. Sannan akwai tarin kayan ƙere-ƙere, na gilashi, da duwatsu da kayan kwalliya, da kayan ƙarafa na yumɓu, da kuma manyan katifu na Turai, waɗanda kayan tarihi ne da ba safai ake samunsu daga bangarorin duniyar Musulunci ba.

Takubban Annabi Muhammad da kuma gidajensu, da fitattun makera na zinare na Daular Usmaniyya suka yi wa wurin sanyawa, wannan hoton an dauke shi ne a ranar 3 ga watan Yulin 2018 a Turkiyya
Bayanan hoto,Takubban Annabi Muhammad da kuma gidajensu, da fitattun makera na zinare na Daular Usmaniyya suka yi wa wurin sanyawa, wannan hoton an dauke shi ne a ranar 3 ga watan Yulin 2018 a Turkiyya

Wannan wata tasa ce, da aka yi imanin cewa Annabi Mohammed ya sha ruwa da ita, tana ɗaya daga cikin abubuwan da aka baje kolinsu a Fadar Topkapi da ke Santambul
Bayanan hoto,Wannan wata tasa ce, da aka yi imanin cewa Annabi Mohammed ya sha ruwa da ita, tana ɗaya daga cikin abubuwan da aka baje kolinsu a Fadar Topkapi da ke Santambul

 

Hajrul Aswad, ko Baƙin Dutse da aka nuna a fadar Tokpati a ranar 3 ga watan Yuli na shekarar 2018
Bayanan hoto,Hajrul Aswad, ko Baƙin Dutse kenan, wanda ke da matuƙar muhimmanci ga musulmin duniya, an nuna shi a fadar Tokpati a ranar 3 ga watan Yuli na shekarar 2018

 

Mazubar ruwan Ka'aba kenan, wadda ita ma ka'aba kamar yadda aka sani ta na matukar muhimmanci ga al'ummar musulmin duniya, an nuna ta ne a fadar Topkapi Palace a ranar 3 ga watan Yuli na shekarar 2018
Bayanan hoto,Mazubar ruwan rufin Ka’aba kenan, wadda ita ma ka’aba kamar yadda aka sani tana da matuƙar muhimmanci ga al’ummar musulmin duniya, an nuna ta ne a fadar Topkapi a ranar 3 ga watan Yuli na shekarar 2018

Gashin gemun Annabi Muhammad, da Hatiminsa da wasikunsa, da takubban Annabi Muhammad da gidajensu, na cikin wasu wuraren ajiya na musamman da maƙeran daular Usmaniyya suka samar, kuma ana nuna su ga dumin masoya Annabi Muhammad na duniya da mabiyansa, da kuma wasu sauran kayayyaki da ake alakantawa da shi.

Silin gashin gemun Annabi Mohammed kenan, wanda ke da matuƙar tsarki ga al'ummar musulmi shima an nuna shi ne a Fadar Topkapi.
Bayanan hoto,Silin gashin gemun Annabi Mohammed kenan, wanda ke da matuƙar tsarki ga al’ummar musulmi shima an nuna shi ne a Fadar Topkapi

Rahoton BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.