Wata matashiya wadda ba’a bayyana sunanta ba ta bayyana irin muguntar da mahaifiyarta ke yi domin samun kwastomomi a gidan cin abincinsu.
Kamar yadda matashiyar ta shaida, mahaifiyarta tana amfani da ruwan gawa wajen shirya abincin da take sayarwa, sannan kuma tana binne wasu sassan jikin mutane a kusa da harabar gidan abincin.
Ta kuma bayyana cewa mahaifiyarta tana tafiya Togo duk bayan kwana 21 don yin sadaukarwa ga abin bautar da take yi don ci gaba da bunƙasa kasuwancinta.
Matashiyar da ke cikin damuwa wacce ta bayyana laifinta mamarta sosai a rubuce-rubucenta ta kara bayyana cewa tana tausaya wa kwastomomin mahaifiyarta saboda yawancinsu sun talauce bayan sun fara cin abinci a gidan abincin na su.
Matashiyar ta ce ba ta son fara yin irin munanan ayyukan da mahaifiyarta amma muguwar uwar ta dage akan idan bata bi sawunta ba, babban bala’i zai afka wa dangi.