fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Hotuna: Matar tsohon shugaban kasa, Patience Jonathan ta kaiwa A’isha Buhari ziyara a fadar shugaban kasa

Mai dakin shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta gana da matar tsohon shugaban kasar Patience Jonathan inda suka tattauna kan babutuwa da dama.

Wata sanarwa da Aisha Buhari ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce Patience Jonathan ta kai mata ziyara a fadar shugaban kasar da ke Abuja ranar Litinin.
“Mun tattauna kan yunkurina na ganin mata sun kara shiga harkokin siyasa da kuma gudanar da harkokin mulki a kananan matakai,” in ji Aisha Buhari.
A makon jiya ma, mai dakin tsohon shugaban kasar, Turai Yar’adua ta kai ziyara wurin Aisha Buhari inda suka tattauna kan cin zarafin mata da shan miyagun kwayoyi.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Hotunan zakakuran matasan lauyoyi da suka kare wanda ake zargi da kashe Deborah Sokoto


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.