fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Hotuna: Ministan sadarwa Dakta Isa Ali Fantami a lokacin da yake ganawa da Bankin Duniya, Gwamnonin Najeriya ta Kwamfuta

Ministan sadarwa Dakata Isah Aliyu Fantami a waddanan hotunan a yayin da yake ganawa da bankin duniya ta hanyar kwamfuta da fasahar zamani.

 

Ganawar tasu ta kasancene kan rawar da Fasahar Zamani zata taka wajan yakar annobar cutar Coronavirus/COVID-19 .

 

Ministan dai ya jima yana jawo hankali kan amfani da fasahar zamani wajan ganawa musamman a lokacinnan da ake fama da cutar Coronavirus/COVID-19.

 

Ministan ya kuma gana da kungiyar gwamnoni inda itama ganawar ta kasance ta kwamfuta wadda suka tattauna yanda za’a yi amfani da fasahar zamani wajan gano ainahin masu bukatar agajin gwamnatin tarayya dan a basu tallafin kyautata Rayuwarsu.

Karanta wannan  Gwamnatin jihar Ondo zata baiwa duk wanda ya kawo mata labaran sirri na 'yan bindiga naira dubu hamsin

 

Ministan ya kuma jawo hankalin gwamnonin wajan amfani da damar fasahar sadarwa wajan ganawarsu da kuma hada hannu dan kawowa Najeriya ci gaba ta fannin fasahar Zamani.

 

 

Ministan ya kuma yi irin wannan ganawa da da wakilan kamfanin Huawei.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.