fbpx
Friday, February 26
Shadow

Hotuna: Mutane da yawa sun jikkata, an lalata motoci a yayin artabu tsakanin magoya bayan Okorocha da Uzodinma a Imo

Mutane da yawa sun jikkata kuma motoci da yawa sun lalace sakamakon rikici tsakanin magoya bayan tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, da magoya bayan gwamnan jihar mai ci, Hope Uzodinma, a Royal Spring Palm Hotels and Apartments dake Akachi, Owerri a ranar Lahadi 21 ga Fabrairu.

A ranar Juma’ar da ta gabata, Kwamishinan Filaye na jihar, Enyinnaya Onuegbu, ya jagoranci wasu mambobin kungiyar da ke jihar don kwace kadarorin da aka ce na Nkechi ne, matar matar Okorocha.

A yammacin yau, tsohon gwamnan ya jagoranci wasu daga cikin magoya bayan sa suka je da karfi domin su kwace otal din.

Wannan ya bakantawa magoya bayan gwamnan mai ci, Inda nan take fada ya barke wanda ya kai ga wasu daga cikinsu suka samu raunuka daban-daban tare da lalata motoci a yayin arangamar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *