fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Hotuna: NDLEA ta kama masu safarar hodar Iblis

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta kama masu safarar kwayoyi a filin jirgin sama na Murtala Muhammad dake Legas.

 

Kwayar ta wani dan shekaru 52 ne dake kasar Brazil amma dan Asalin jihar Imo me suna Akudirinwa Hilary Uchenna.

 

Yace shima dai kwayar ba tasa bace, bashi aka yi ya kawo Najeriya da alkawarin za’a bashi Miliyan 5 idan yayi nasarar shigowa da ita Najeriya.

Hakanan a filin jirgin sama na jihar Enugu ma an kama wani dan shekaru 37 da ya dawo daga kasar Afrika ta kudu, Ezekwesili Afamefune.

Karanta wannan  PDP ta bukaci gwamnatin shugana Buhari ta gudanar da bincike akan tsohon shugaban soji, janar Burtai kan satar kudin makamai daya yi

 

Shina ya shigo da kwayoyi amma dubunsa ta cika.

Hakanan akwai Christian John, Chibuzor Uba, Stanley Chibuzor, da Oluwaseun Agboola da aka kama duk suna safarar miyagun kwayoyi, kamar yanda kakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi ya tabbatar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.