Shugaba Muhammadu Buharai ya kai ziyara jihar Kano fadar mai martaba sarki Alh. Aminu Ado Bayero inda yayi ta’aziyya ga iyalan mutanen da gas ya kashe a jihar.
Gwamna Ganduje da sauran manyan mutanen jihar sun hallacin fadar yayin mai martaba Sarki ya jinjinawa shugaba Buhari sosai bisa ziyarar tasa.
Kuma shima Ganduje ya bayyana cewa an samu tallafi kudi da za’a baiwa iyalan mutanen da wannan al’amarin ya faru dasu.
Buhari ya bayyana cewa yana mika sakon ta’aziyya da mutanen da suka rasu kuma yana fatan masu jinya zasu warke nan bada dadewa ba.
