fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Hotuna: Ta mutu bayan An mata fyade a coci

Wata matashiya me kimanin shekaru 22, Uwaila Omozuwa ta mutu a jihar Edo bayan da wasu da ba’a san ko su waye ba suka mata fyade suka kuma mata dukan kawo wuka da yayi sanadin Mutuwarta.

 

Matashiyar dalibace dake ajin farko a Jami’ar Benin kuma ta bayyana cewa ta je karatune a cocin Redeem Christian church of God dake Benin.

Lamarin ya farune ranar 27 ga watan Mayu inda ta wani dake kula da cocin ya je dauko makulli ya kulleta sai aka gaya masa cewa akwai mutum a ciki, ko da ya leka sai yaga yarinyar cikin jini, an yi amfani da abin kashe wuta an daketa, sun yi tsammanin ta mutu amma daga baya aka kaita Asibiti.

Karanta wannan  Tekun Legas ya tafi da dalibai hudu da suka je murna bayan sun lashe jarabawar WAEC

 

Ta bada labarin cewa tana karatune wasu da bata san ko suwaye ba suka shiga cocin suka daketa tare da yi mata fyade.

 

Ta dai mutu a jiya Asabar a Asibitin kiyarwa na jami’ar Benin din wanda hakan ya jawo Allah wadai da lamarin da kuma kiran cewa a dauki mataki kan lamarin a shafukan sada zumunta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.