Mijin tsohohuwar ‘yar majalisa, Mrs Sharon Aondona Daboh watau David Kersha Fiase ya kai kara wajan ‘yansanda inda yace matar zata kasheshi.
Yayi rokon cewa a raba aurensu kamin ta kaishi kiyama.
Ya kara da cewa, duk wata karamar matsala da suka samu, matar bata daga masa kafa. Yace kai ta kai ga har saids ya tsere daga gidansa dan tsoron matar.
A lokacin da ya kaiwa kotu korafin, kamin a kaiwa Sharon takardar sammace, wasu bata gari suka tareshi suka masa danbanzan duka.
Dan haka lauyansa yace suna neman a raba auren