Wata mata ‘yar shekara 75 ‘yar jihar Delta ta samu nasarar haura igiyar NEPA zuwa ga baban injin da ke tace wutan lantarki na haitanshan, ta sake haɗa wutar lantarkin biyo bayan lokacin da aka yanke mata wutar
Wannan tsohuwar ta maida wannan wutar lantarki a bainar al’umma, bayan da Kamfanin Power Holding Company ya yanke da kanta, ita kuma matar ta hau babu ko wani alaman kayan aiki, ta saka hannunta ga cikin wayoyin wutan mai nau’oin kalan dalma ta gyara wutan lantarkin ras kamar yadda ganau ya tabbatar mana da hakan.

“Saukowarta ba wuya, nan take jama’a suka shiga mata tafi, mai sautin raf-raf-raf tare mata jinjina da Tayi dako wasu nefan baza su iya wannan bajintar da Tayi ba, ta kuma ce taga wadda zai zo ya kara yanke wutan lantarkin.” Inji wani ganau da ido.