fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Hotuna: Wani yaro ya gamu da Ajalinsa bayan da wani Direban mota ya bugi shi

Al’amarin dai ya faru ne a jihar Anambra inda wani Direban Mota wanda aka gaza bayyana sunan sa yayi Awon gaba da wani karamin yaro a sanadin tsananin gudu da Dirban motor ke yi akan titi.

Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 2 na ranar Talata a dai-dai lokacin da yaron yayi kokarin tsallaka titi inda Dirban motar yayi ciki dashi kamar yadda wasu majiyoyi suka shaida faruwar lamarin.

Bayan kokarin ceto yaron amma ina lokacin da aka isa dashi zuwa Asbiti tuni rai yayi halinnasa kamar yadda hukumar Kiyaye hadura ta tabbatar da al’amarin.

Suma wasu Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa, hatsarin ya faru ne a sakamakon gudun wuce sa’a da Direban da ake zargi yake yi akan titi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.