fbpx
Friday, June 9
Shadow

Hotuna: Wata mata da bata san tana da ciki ba ta haihu a bandaki, kadan ya hana dan ya fada masai

Wata mata da bata san tana da ciki ba ta haihu a bandaki inda hakan yasa ta kusa kora ruwa akan dan nata.

 

Matar bata ma san ta haihu ba, sai da ta tashi tsaye zata kora ruwa, sai ta ga hannun jariri a cikin bayin.

 

An kai Lalene Malik Asibiti bayan data fara korafin cikinta na ciwo.

 

Matar tasha maganin hana haihuwa kuma an mata gwajin ciki wanda ya nuna cewa bata da ciki, hakan yasa ta yi tunanin ciwon ciki ne kawai ke damunta.

 

A karshe dai ta haihu kuma dan yana cikin koshin lafiya.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *