Wannan kyautatawar an yi ta ne karkashin jagorancin Dr Abdulkadir Aliyu Shinkafi Likitan Gwamna da Aliyu Usman da Bilyaminu Maradun da suransu.
A koda yaushe Gwamnan ya auna yakan bada kudaden don zagawa cikin gaari don rabawa al’umma kudin dai duk wanda Allah ya ciyar yana samun naira dubu 50,000 wasu kuma 20,000 wasu 10,000 ya danganta da sana’ar da mutum yake yi.
Al’umma sai godiya kawai suke yi ga Maidaraja Gwamnan Zamfara akan wannan kulawar da yake ba su na ganin sun samu jari sun dogara da kansu.
