fbpx
Monday, August 15
Shadow

Hotuna: ‘Yan Bindiga sun kai hari Kaduna, sun sace wannan matar da danta da kuma wasu 34

Akalla mutane 36 ne rahotanni suka bayyana cewa, ‘yan Bindiga suka sace a Keke B dake millennium city, a karkashin karamar hukumar Chukun dake jihar kaduna a daren jiya.

 

Wasu shaidu sun bayyana cewa gida-gida ‘yan Bindigar suka rika bi suna daukar mutane, kuma sun kwashe akalla awanni 2 suna wannan aika-aika.

 

Daily Trust ta ruwaito cewa ba wani cikin dare bane sosai abin ya faru, irin wajan karfe 8:30 ne kamar yanda wani mazaunin yankin ya fada mata.

 

Wani bakanike ya samu ya tsere daga hannunsu, amma sun samu sun tafi da mutane 36.

 

Zuwa yanzu dai babu sanarwa a hukumance daga jami’an tsaro a jihar ta Kaduna kan wannan harin.

Tuni dai ‘yan uwa da abokan arziki suka fara hawa shafukan sada zumunta suna nuna Alhini kan wadanda aka sace da yi musu addu’ar fatan Allah ya kubutar dasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.