Sunday, June 7
Shadow

Hotuna: ‘Yan kasuwar Kaduna sun yiwa dokar gwamnati biyayya

Kasuwannin ceceniya/Sheikh Abubakar Gumi duk a kulle, ‘yan kasuwar Bacci ma basu fito ba.

 

Masu sufuri, motoci da babura da tafiya ciki da wajen Kaduna na ci gaba da aiki.

 

‘Yan kasuwar sayar da kayan Mota sunce suna tunanin bandasu.

 

Bankuna na aiki.

 

Shafin hutudole ya zagaya cikin garin Kaduna dan duba yanda sabuwar doka me tsauri da gwamnatin jihar ta saka dan kare yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19 ke aiki.

hutudole.com hoton kasuwar Kaduna
Hoton kasuwa

A jiyane dai gwamnatin jihar Kadunan ta saka dokar kulle kasuwanni in banda masu sayar da abinci da magunguna sannan ta baiwa ma’aikata daga mataki na 12 umarnin zama a gida nan da kwanaki 30.

 

Gwamnatin ta kuma ce zata tursasa dokar hana taruwar jama’a da yawa wadda a farko ta bada shawara amma wasu suka ki bi. Sannan za’a kulle makarantun islamiya dana Allo.

 

A cikin Garin Kaduna, jama’a da yawa sun bi wannan doka dan kuwa akwai karancin zirga-zirgar ababen hawa ba kamar yanda aka saba.

hutudole.com masallacin sultan Bello
Hoton titin Masallacin Sultan Bello

Manyan titunan Cikin Garin Kaduna, irinsu Zaria Road, Ali Akilu Road, Ahmadu Bello Way akwai zirga-zirgar Ababen hawa amma ba kar yanda aka saba ba.

 

‘Yan kasuwa na gefen kasuwar Bacci duk basu bude ba, wasu sun fito suna tsaye a bakin shagunan amma basu bude ba.

 

A zantawar da Hutudole yayi da wasu daga cikinsu, sun bayyana cewa sun bi wannan doka amma suna jira suga yanda zata kaya idan akwai halin bude shagunan.

 

Kasuwar Ceceniya da Sheikh Abubakar Gumi ta kasance a kulle inda jami’an tsaro ke tsaron kofofinta.

 

Babu wasu jami’an tsaron dake tursasa bin wannan doka amma kuma jama’a na mata biyayya daidai gwargwado.

 

A cikin sanarwar ta jiya gwamnati ta bada shawarar takaita zirga-zirga da tafiye-tafiye idan ba na dole ba ko na laruri.

hutudole.com hoton kasuwar bacci
Shagunan Kasuwar Bacci a Rufe

Saidai masu aikin sufiri, Motoci da babura da Keke Napep, Adaidaita sahu suna ci gaba da aiki. Hakanan tashoshin motocin Kawo, dana babbar kasuwa dana Kasuwar bacci duk sun tabbatarwa da Hutudole cewa suna lodi zuwa garuruwa sannan kuma ana shigowa. Saidai a Kawone muka samu rahoton cewa matafiya sun ragu ba kamar da ba.

hutudole.com hoton Oriagwata dake Kaduna
Yara na kwallo akan Titin Calabar Street

A ta bangaren masu sayar da kayan mota kuwa, Calabar Street, Katsina Road, Benin da sauransu suma dai basu fito ba kamar da sannan akwai takaitar zirga-zirgar ababen hawa inda har ma yara na kwallo a tsakiyar Titi.

 

Da hutudole ya tambayi wasu daga cikin wanda suka bude shaguna sunce”mu kasuwa muka ji ance, ba mu tsammanin hadda mu”.

hutudole.com hoton kasuwar Sheikh Abubakar Gumi dake Kaduna
Kofar shiga kasuwar Sheikh Gumi ta wajan bakin Dogo

A babbar kasuwa kuwa duk manyan shaguna irin su Mangal da Kura da Makarfi yawanci a kulle suke. Hakanan kasuwar wayoyi ta Royal da ta saba da cinkoso itama a kulle take. Mun zanta da wani inda yace suna wa dokar biyayya kuma zasu ci gaba da mata biyayya har abinda hali yayi.

hutudole.com hoton kasuwar waya ta Royal dake Kaduna
Kasuwar Waya ta Royal ba kowa

Ta bangaren masu sayar da abinci kuwa duk sun fito suna cin kasuwarsu ba babbaka.

Bankuna sun bude sannan mutane na tururuwar zuwa ATM.

 

A zantawar da hutudole yayi da wasu sun bayyana cewa basu yadda akwai cutarnan a Najeriya ba amma sun bayyaja aniyrmar bin dokar da gwamnati ta saka.

 

Saidai da dama sun ce ba zasu daina zuwa Sallah ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *