Friday, May 29
Shadow

Hotuna: ‘Yan Sanda A kasar Kenya sun kama Mutumin da yayi amfani da Gam ya rufe Al’aurar Matarsa

‘Yansanda a kasar Kenya sun bayyana nasarar kama wani magidanci me kimanin shekaru 30 da yayi Mafani da Sufa Gulu ya rufe al’aurar matarsa.

 

James Kifo Muruiki ya aikata wannan laifine a Ranar 16 ga watan Mayu saidai bayan da matar tasa ta kai kara wajan ‘yansanda sai ya shiga buya.

Hukumar dake binciken mayan laifuka ta kasar Kenya ta bayyana cewa, a karshe dai an kama mutumin kuma bayan kammala bincike za’a gurfanar dashi a gaban kuliya.

 

Tace yanda ya aikata laifin shine, ya ja matarsa can bayan gari cikin dare inda ya sakata ta yi tsirara sannan ya fara tambayarta maza nawa ta yi lalata dasu lokacin baya nan?

Da taki gaya masa shine ya mata dukan kawo wuka, ya saka mata yaji, Gishiri da gam din super Gulu a al’aurarta inda yayi amfani da wuka ya tura mata su.

 

Ya kuma rufe mata baki da kunne inda ya tafi ya barta nan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *