fbpx
Friday, February 26
Shadow

Hotuna: Yan Sanda Sun Kama Wani Matsafi Da sassan jikin dan Adam

Yan sanda a jihar Osun a ranar Talata sun kama wani mutum, Moshood Anifanikun, da sassan jikin mutum a gidansa da ke yankin Gbongan.

Daya daga cikin makwabtan wanda ake zargin ya ce warin da ke kusa da gidansa ya kawo shakku kuma mazauna garin sun sanar da ’yan sanda.
Ya ce ‘yan sanda sun gano sassan jikin mutane da ke rubewa lokacin da suka binciki gidansa don haka suka kama mutumin.
Wani mazaunin garin ya tabbatar da shaidar farko, yana cewa, “Ba mu san inda Moshood ya samo sassan jikin mutum ba. Kawai sai muka ji warin kuma muka tambayi matar sa meye ke wari a gidan su.
“Lokacin da Moshood ya fahimci cewa muna zargin sa, sai ya dauki jakar daga dakin ya ajiye ta a bayan gida. A nan ne ‘yan sanda suka gano shi. ” Wanda ake zargin ya furta cewa ya ciro sassan mutane ne daga cikin kabari.
Kakakin ‘yan sanda na jihar, Yemisi Opalola, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce za a bincika lamarin sannan a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *