Wadannan hotunan Birnin Wuhan dake kasar Chinane inda Annobar cutar Coronavirus/COVID-19 ta bulla wadda ta karade Duniya.
Mutanen Birnin sun gudanar da wani shagali inda Dubban Mutane suka taru akai ta wanka tare a wani kudiddifi.
Lamarin ya farune ranar 15 ga watan Augustan da muke ciki tin bayan dage dokar kulle da aka saka a garin har zuwa yanzu babu wanda aka kara samu ya kamu da cutar.