fbpx
Saturday, September 19
Shadow

Hotuna:Abdulmumin Jibrin yayi ziyarar bankwana da Ofishin kasuwancinsa bayan da shugaba Buhari ya bashi sabon mukami

Ya Rubuta a shafukansa na sada zumunta kamar haka:

 

Nada ni a matsayin Babban Darakta a Hukumar Gidaje ta Kasa

Zan sake tafiya hutu na wani lokaci daga harkokin kasuwanci. Na yi tunanin zan dade a wannan lokacin a Kamfani na. GreenForestGroupLTd.

Bayan kwashe kusan shekara 10 a majalisa, nadin da Shugana Kasa Muhammadu Buhari ya min a matsayin Babban Darakta a Hukumar Gidaje ta Kasa ya kashe min kishin ruwan da nake shi na komawa aiki a bangaren zantarwa.

Ina so in yi amfani da wannan damar wajen yin godiya ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bisa amincewa da ya yi da ni da kuma danka min wannan amanan

Sannan ina mai tabbatar masa cewa ba zan zuba masa kasa a ido ba. Zan yi aiki tukuru tare da hadin gwiwar abokan aikina na Sanata Gbenga Ashafa da Ministan Ayyuka Babatunde Fashola wajen cimma nasarorin hukumar.

Ina kuma mika godiya ga Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje bisa gudunmuwarsa wajen samun wannan matsayin. Ina kuma yiwa jamaar kano da kiru da Bebeji godiya bisa aduoi da suka yi mana tare da fatan alheri.

 

Ina mai bukatar addu’o’inku wajen sauke wannan nauyin a daidai lokacin da nake shiga wani sabon bangaren aikin. Allah saka da alheri.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwx



Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *