Tauraron mawakin Hausa, Ali Isa Jita ya sanar da budewa matarsa, Asibiti a Kano.
Jita ya bayyana cewa Asibitin shine burin matarsa shiyasa yayi kokarin ganin ya bude mata shi. A sakon da ya fitar ta shafinsa na sada zumunta, Jita ya bayyana cewa yana godiya ga duka wanda suka je dan tayashi Murna.