Tauraron mawakin Gambara, DJ Abba kenan a wadannan hotunan yayin da ya kaiwa tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar ziyara a Yola.
DJ Abba ya je Yola wasa ne inda kuma a cikin hotunan aka ganshi tare da daya daga cikin ‘ya’yan Atiku Abubakar, Shehu Atiku.
DJ Abba ya saka hotunan a shafinshi na sada zumunta inda yakewa Shehun godiya.
