Wednesday, December 4
Shadow

Hotuna:Hadiza Gabon ta bayyana ainahin shekarunta yayin da take murnar zagayowar ranar haihuwarta

Tauraruwar Fina-finan Hausa, Hadiza Gabon ta yi murnar zagayowar ranar haihuwarta inda tace ta cika shekaru 35.

Hadiza ta bayyana hakane a shafinta na sada zumunta inda kuma masoya da abokan arziki suka yi ta tayata murna.

Da yawa dai masu murnar ranar haihuwarsu basu cika bayyana shekarunsu ba, amma Hadiza Gabon ta yi ta maza ta bayyana cewa shekarunta 35.

Ko da yake a hakan ma wasu da yawa sukan karyata.

Daga cikin abokan aikin Hadiza Gabon:

Shamsu Dan iya ya tayata Murna inda ya saka hotonsu tare a shafinsa da yi mata fatan Alheri:

Sauran wanda suka taya Hadiza Gabon murna sun hada da Dj Abba, Hassan Giggs, da dai sauransu.

Karanta Wannan  Kalli kayatattun Hotuna daga wajan bikin zagayowar ranar haihuwar Hadiza Gabon

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *