Rahotanni sunce a jiya, Laraba, ‘yan Bindigar da ake kira da wanda ba’a sani ba amma ake kyautata zaton ‘yan kungiyar IPOB ne dake son kafa kasar Biafra sun kai hari kan kasuwar Nkwo Ibagwa dake karamar hukumar Igbo-Eze South ta jihar Enugu.
‘Yan bindigar sun rika harbi a iska wanda yayi sanadiyyar kisan wannan matashin da hotonsa ke kasa.
‘Yan uwa da abokan arziki da yawa sun koka da rashin wannan matashi da aka yi inda da yawa suka hau shafukan Facebook suke alhinin rashin matashin.
Hakanan rahoton Sahara Reports yace ‘yan Bindigar sun kona kayan ‘yan kasuwa da motoci wanda aka yi kiyasin sun kai na miliyoyin Naira.