Wani magidanci da ya zargi matarsa sa cin amanarsa ya kashe ta sannan ya kashe kansa ta hanyar rataya.
Lamarin ya farune a Bashua, dake Karamar hukumar Boki ta jihar Cross-River inda. Martmercy Busaosowo ta bada labarin cewa, lamarin ya farune da safiyar jiya, Litinin inda mutumin ya kashe matarsa.
An bazama nemansa kawai sai shima aka ga gawarsa rataye a jikin bishiya.

