fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Hotuna:Masoyan Buhari na tururuwar Turawa Rarara Dubu 1

Ga dukkan Alamu ba kamar yanda wasu musamman ‘yan hamayya da wanda suka sauka daga motar goyon bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari ke tsammani ba, har yanzu akwai ‘yan gani kashenin shugaban kasar.

A jiyaje shahararren mawakin shugaban kasar, Dauda Kahutu, Rarara ya bayyana cewa yana neman masoya shugaban kasar su tara masa kudi ta hanyar aika Naira Dubu 1 kowannensu.

 

Wannan bukata ta Rarara ta tada kura inda wasu ke cewa sam ba zasu iya ba, wasu kuwa na cewa ko nawane zasu tura, kai wani ma ya bayyana cewa ko dubu 50 ne zai tura.

Karanta wannan  Kwankwaso so yake yayi anfani da farin jinin Peter Obi don ya lashe zabe mai zuwa, cewar darektan kamfa na Peter Obi

 

Saidai yayin da wasu ke fada da baki, wasun kuwa tuni suka fara turawa Rarara wannan kudi inda suka saka hotunan shaidar hakan kamar yanda za’a iya gani a kasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.