fbpx
Wednesday, May 25
Shadow

Ali Nuhu, Nafisa Abdullahi da Ramadan Booth a filin wasa na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dake Ingila

Taurarin fina-finan Hausa, Ali Nuhu(Sarki) Nafisa Abdullahi da Ramadan Booth kenan a filin wasa na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Stamford Bridge dake kasar Ingila inda aka buga wasa tsakanin Chelsean da Manchester United a jiya Lahadi, Jaruman sunje kallon wannan wasa inda aka ga alamun farin ciki da murnar su a cikin hotuna da bidiyon da suka dauka lokacin suna cikin filin.

A shekaran jiyane dai aka kartama jaruman da lambar yabo wadda jaridar African Voice ta basu kuma shine makasudin zuwansu kasar Ingilar karkashin rakiyar Ali Nuhu, sunyi amfani da wannan dama inda suke ziyartar gurare da dama dan kashe kwarkwatar ido.

Leave a Reply

Your email address will not be published.