fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Hotunan Ban Tausai:’Yan sanda sun kama malamin da ya yi wa almajiransa mugun duka

‘Yan sanda sun kama wani malamin makarantar allo a jihar Diffa da ke kudu maso gabashin jamhuriyar Nijar bayan an zarge shi da yi wa almajiransa dukan kawo wuƙa.

 

 

Tuni dai, mahukunta suka kwashe almajiran inda suka kai su asibiti. Bayanai dai sun ɗaliban suna can kwance suna shan magani.

 

 

Mazaunan garin Diffa sun riƙa yaɗa wasu hotuna a shafukan sada zumunta da ke nuna wasu ƙananan yara tuɓe babu riguna, wasu daga ciki an ga bayansu duk a farfashe da alamun duka.

 

Yayin da wasu kuma dukan har ya shafi fuskokinsu, ga kuma baki a kukkumbure.

 

 

Wani shaida da ya zanta da BBC kan wannan lamari, ya ce yana cikin tafiya wani yaro ya taho da gudu yana neman agaji daga gare shi. “Na ga gudan ba kyau, (halin da yake ciki)”.

 

Shaidan wanda bai bayyana sunansa ba ya ce ko da ya riƙe yaron da ya tunkare shi da farko, yana ƙoƙarin neman mota don kai shi asibiti, sai suka hango sauran yaran na tahowa.

Karanta wannan  Da Dumi Dumi: Shugaban karamar hukumar mahaifar Atiku Abubakar ya koma jam'iyyar NNPP

 

A cewarsa ko da ya tambaya, sai aka bayyana masa cewa malaminsu ne ya rufe su cikin wani gida ya yi duka saboda sun yi masa laifi.

 

“Malaminsu ya yi bulaguro, da ya tafi ya dawo, sai anka kawo mai kashedi a kan almajiran nasa, lamarin da ya sa ya yi ta dukansu ke nan,” in ji wannan shaida.

 

 

Ya ce bayan sun tuntuɓi hukuma ne, sai ‘yan sanda suka je suka kwashe ɗaliban tare da kama malamin nasu daga bisani.

 

 

Hukumomi a jamhuriyar Nijar dai sun ce ba su laminci irin wannan al’amari na cin zarafin ƙananan yara ba.

 

 

Daraktan kula da addinai a ofishin ministan cikin gida, Abdulsamad Yahya ya ce yanzu haka akwai dokar da aka ɓullo da ita a Nijar wadda ta yi tanadi kan yadda malaman allo za su yi mu’amala da almajiransu.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.