
A lokuta da dama aiki yakan tashi, kodai gwamnati ko kuma wani kamfani ko kuma wani hamshakin attajiri zaiyi wani gini kuma ginin yana bukatar a sayi gidajen mutane, su tashi dan a yishi, koda anan Najeriya haka na faruwa, to saidai ana samun wasu musamman a kasashen ketare da suke kekashe kasa suce sufa sam ko nawa za’a basu ba zasu taba sayar da gidansu ba.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Irin wannan ne yasa aka hada wannan labari na masu gidaje da suka ki sayar da gidajensu a lokacin da bukatar yin wani aiki ya taso da zai bi ta kan gidan nasu.
Wannan hoton na sama wani gidane a kasar China da masu gidan suka kekashe kasa sukace sam ba zasu sayar dashi ba a lokacin da gwamnatin kasar zata gina titi wanda dole sai yabi ta kan gidan nasu. Dole haka gwamnatin ta sayi sauran gidaje tabar musu nasu kwallin-kwal aka kuma gina titin ya saka gidan a tsakiya.
Daga baya masu gidan sun tashi amma duk da haka gwamnati bata rushe gidan ba, an barshi a tsakiyar titi dan ya zama abin tarihi.

Wannan shima wani titine a garin Guangzhou na kasar china wanda da aka tashi ginashi, ana bukatar yabi ta kan wasu gidajen al’umma, anyi tsada da saura sun tashi amma wasu mutum uku suka kekashe kasa sukace sam ba zasu sayar da nasu gidajen ba, dole aka kyalesu kuma hakan tasa aka yiwa titin wannan irin shatale-tale haka sai abin ma ya zama gwanin ban sha’awa.

Wannan ma wani gidane a Austin Spriggs dake kasar Amurka wanda shima da farko me gidan yaki sayarwa a lokacin da ake bukatar ya sayar a gina wasu dogayen gidaje bayan makwautanshiduka sun sayar, da farko dai an bashi kudi dalar Amurka miliyan 3 amma yaki sayarwa, daga baya da aka kara yakai miliyan hudu, sai ya sayar.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Wannan shima gidan wata matane da aka tashi gina wasu benaye, magwabtanta suka sayar amma ita taki sayarwa duk da an bata kudi har dalar Amurka miliyan daya, dalilin wannan abu da tayi har fim se da aka kwaikwayi labarinta akayi dashi.

Wannan dan tsukukun gidan na tsakiyar benayennan shima na wata matane da aka tashi yin ginin benayen, duk makwautanta suka sayar, aka rushe gidajensu amma ita taki sayarwa, dole a haka akayi ginin benayen, abin sai kuma ya bayar da sha’awa.

Shima wannan gida na wata matane a kasar Canada da aka tasi yin sabon gini, na zamani, ta kekashe kasa taki sayar da nata, sai aka rushe na wadanda suka sayar, aka bar mata nata, dan siriri, akayi ginin a haka.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Shima wannan ginin wani mutumne da yake sayar da shayi a ciki a kasar Faransa, da aka tasi yin titi, zai bi ta kan gidan nashi amma ya kekashe kasa yaki sayarwa, dole a haka aka zagaye gidan nashi akayi titin.

Wannan shima wani gidane da me gidan yaki sayarwa duk da an tsara gadar sama zata bi takan gidan kuma makwabtanshi duk sun sayar, a haka akayi ginin gadar kuma yaci gaba da zama a ciki.

Shima wannan gidan wani mutumne a kasar China dake yankin Jiangsu da aka tashi gina gidajen masu kudi, duk makwautanshi suka sayar amma shi yaki, a haka dole akayi ginin.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Itama wannan matar me kiwan kaji, a lokacin da aka tashi gina wata hanya an sayi duk gidajen dake makwabtaka da ita amma ita taki sayarwa da gwamnati nata gidan, dole haka aka kyaleta ita daya a gefen titi, tana ta kiwan kajinta, a gefen dan gidanta.

Shi kuma wannan wani ginine da ya tashi za’a yishi kakan wani kabari, ‘yan uwan mamacin dake kasar China sunki yarda su sayar dashi, saida aka kwashe watanni ana ta ja-in-ja dasu sannan suka hakura aka biyasu aka kawar da kabarin aka cigaba da gini.

Shima wannan gidan wata matane a kasar China da aka tashi yin gini, duk makwautanta suka sayar amma ita saida aka kwashe shekaru 3 ana ta fama da ita sannan ta yarda ta sayar da nata gidan.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Shima wannan ginin a birnin Shanghai na kasar China, masu shi sunki yarda su sayar a lokacin daginin titi zai bi ta kanshi, dole a haka aka gina titin.

Shi kuma wannan ginin a kasar China wani kamfanine ya sayeshi amma wasu mutane, ‘yan haya suka ki tashi daga ciki, kamfanin ya gina rami a kusa da gidan dan ya tilastawa ‘yan hayar su tashi su bashi guri ya cigaba da aiki.

Shima wannan wani gidane da meshi yaki sayarwa duk da mahukunta suna bukatar suyi titi da zaibi takan gidan nashi a kasar China.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Wannan ginin wani mutum ne da aka bukaci ya sayar za’a gina benaye na zamani amma ya kekashe kasa yaki yarda, daga baya dole akayi ginin a haka.

Wannan gonar wasu mutane ce da aka bukaci yin filin jirgin sama da zaibi ta cikinta amma suka ki sayarwa dole aka kyalesu aka gina filin jirgin saman a haka, koda yaushe suna jin kara da jijjigar kasa.

Wannan shima ginin wata matane da taki sayarwa bayan duk makwautanta sun sayar, duk da an yake mata wuta da ruwa amma taci gaba da zama a gidan a haka, matarce tsaye a jikin wannan hoton, ga gidan nata can yana kallo.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Wannan shima wani mutum ne a kasar China da aka bukaci ya sayar da gidanshi za’a gina wasu shagunan saide-saide amma yaki, a haka akayi ginin, ga didan nashi nan a gaban shagunan.

Wannan shima za’a gina titine wanda zai bi takan gidanshi amma yaki yarda ya sayar da gidan nashi, a haka aka fara ginin titin.