Tauraruwar fina-finan Hausa Nafisa abdullahi kenan a shahararriyar gadarnan ta birnin landan, Nafisar taje gurin gadar inda ta dauki hotuna hadda gajerun bidiyo kuma tana cikin nitshadi da annashuwa, tayi murnar ganin gadar.
Nafisa tace akwai sanyi a garin sosai, shiyasa duk inda za’a ganta a cikin hotunan sanye take da rigar sanyi.