Hukumar Sojojin Saman Najeriya ta tabbatar da kai mata harin kwantan Bauna wanda yayi sanadiyyar mutuwar wasu sojojin yayin da wasu suka jikkata.
Kakakin Hukumar, Ibikunle Daramola ne ya tabbatar da hakan saidai be bayyana adadinsu ba. Yace amma sojojin sun dakile harin tare da kashe ‘yan Bindigar da dama.
Wasu ‘yan uwa da abokan arziki na sojojin sun shiga shafukan sada zumunta suna alhinin rasuwarsu.