fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Hotunan Yanda aka yi bikin baiwa Yusuf Buhari Sarauta a Daura

An naɗa Yusuf Buhari ɗan gidan Shugaban Najeriya sarautar Talaban Daura a masarautar Daura a ranar Asabar.

Mataimakin Sugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo da Shugaban Majalisar Dattawa ta Najeriya Ahmad Lawan da sauran manyan baƙi, kamar su gwamnan Katsina Aminu Bello Masari da Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero duk sun isa garin Daura domin halartar taron naɗin sarautar da za a yi wa ɗan Shugaba Muhammadu Buhari.

Masarautar ta Daura, wadda ita ce mahaifar Shugaba Buhari, ta naɗa Yusuf Buhari a matsayin Talban Daura kuma Hakimin Kwasarawa.

Sarkin Daura Alhaji Umar Farouk wanda shi ne Sarkin na Daura shi ne ya yi wannan naɗin.

Sai dai ana wannan bikin ne a yayin da shugaban Najeriyar ke Turkiyya inda yake halartar taron cinikayya tsakanin Turkiyya da Afrika.

A wannan shekarar ne Talban na Daura ya auri Zahra Nasir Ado Bayero wadda ƴa ce ga Sarkin Bichi.

Daga BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.