fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Hotunan Yanda akawa wata mata Tumbur saboda satar Rogo

‘Yan Banga a jihar Rivers sun yiwa wata mata me suna Comfort Eze tumbur saboda satar Rogo inda aka rika yawo da ita cikin unguwa sai da kowa ya ganta Tsirara.

 

Yan bangar garin Ovogo na karamar hukumar Emuoha dake jihar ne sukawa matar da ake zargi da sarar rogo wannan aika-aika.

 

Da take gayawa manema labarai yanda lamarin ya faru a hedikwatar kungiyar mata lauyoyi na jihar ta Rivers, Comfort tace sun mata tsirara suka dauki hotunanta suka saka a shafukan sada zumunta. Sannan kuma suka zagaya da ita kowa ya ganta tsirara.

 

Sannan kuma sun nemi ta basu Naira dubu 60 a matsayin diyyar satar da suke zarginta da ita, tace ta biya Naira Dunu 52 amma har yanzu suna neman ta biya sauran Dubu 20.

 

“They tore my clothes, carried me out and blindfolded me; they said they wanted to shoot me to death. They took photographs of my naked body and put them on Facebook and post it everywhere,” the victim spoke in Pidgin English.

Karanta wannan  Bincike ya nuna cewa rabin 'yan Najeriya zasu fada talauci a karshen shekarar 2022

 

Saidai shugaban ‘yan banga na karamar hukumar, Emeka Wori ya bayyana cewa, zasu tabbatar an hukunta me laifi a wannan lamari sannan ita matar an ci zarafinta, ya kara da cewa yanzu DSS sun gayyaci wanda yayi wannan aika-aika.

 

“What happened is an evil act. It was after two days I saw it on WhatsApp, but I could not look at it twice because she (Miss Eze) is my younger sister.

 

“If he (culprit) fails to go to the DSS, we will arrest him and take him there. The first thing is that he has to go and answer the DSS and explain to them why he did what he did.”

 

Hukumar ‘yansandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.