Mutane Miliyan 1.3 ne har yanzu ke fama da matsalar karancin ruwa a yankuna 200 dake jihar Texas ta kasar Amurka.
A ranar litinin, mutane Miliyan 8 ne suka yi fama da rashin ruwan inda a ranar Talata suka ragu zuwa mutane Miliyan 3.4, a ranar Lahadi kuma Miliyan 9 ne suka fada waccan Matsala.
Wannan matsala ta faru ne sanadiyyar tsananin sanyi da aka yi da yayi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 24. Sannan kuma suka fada Duhu saboda rashin wutar lantarki.
