fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Hotunan Yanda Gobara ta tashi a kasuwar Nguru ta jihar Yobe

Rahotanni daga jihar Yoben Najeriya na cewa gobara ta tashi a babbar kasuwar Nguru da ke jihar.

Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana wa BBC cewa gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe takwas na safiyar Asabar.

Sun kuma bayyana cewa gobarar ta tashi ne daga sashen ƴan takalma da kuma ƴan robobi kuma ta laƙume shaguna ba iyaka.

Tuni dai jami’an kai agaji da kuma na kashe gobara suka isa wajen domin kashe gobarar.

Mai magana da yawun ƴan sanda reshen jihar Yobe ASP Dungus Abdulkarim ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin inda ya ce tuni jami’an kashe gobara da matasa suka haɗa hannu inda suke ƙoƙarin kashe gobarar.

Karanta wannan  Gwamnatin tarayya ta sha Alwashin magance matsalar yin kashi a waje

Haka kuma ya tabbatar da cewa ƴan sanda da sauran jami’an tsaro sun isa wurin domin tabbatar da tsaro.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.