LAUYOYI MUSULMI: Wadannan sune zaratan Lauyoyi Musulmai da suka tsaya a Kotu domin ganin sun kare Matasan da aka kama bisa zargin k@$he Deborah (L) wadda tayi batanci ga Annabi Muhammad SAW a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari dake Sokoto.
Muryoyi ta samu rahoto daga Mujallar Sokoto da ta wallafa cewa Lauyoyin na karkashin jagorancin wani Barista Mustapha Abubakar Mada sun nemi Kotu da ta bayar da belin Matasan sai dai Kotun ta dage Shari’ar har zuwa ranar Laraba 18/05/2022 domin duba bukatar belin nasu.
Jaridar ta ruwaito ana tuhumar Matasan ne da laifin hadin-kai wajen cin amana (Criminal Conspiracy) da kuma zuga Jama’a wajen tashin hankali (Inciting Public Disturbance).
Me zaku ce?