Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta kama wata shahararriyar me safarar kwayoyi a jihar Taraba.
Kakakin hukumar, Femi Babafemi ya bayyana cewa, suna bibiyar sahun matar tun a shelarar 2021 amma sai yanzu suka samu kamata.
An kama lamine a kauyen Iware dake karamar hukumar Ardo Kolo ta jihar ta Taraba.