fbpx
Monday, August 15
Shadow

Hukuma ta damke mai maganin gargajiyar daya yiwa yarinya mai tabin hakali da yake lura da ita fyade a jihar Adamawa

Wani mai maganin gargajiya ya yiwa wata yarinya ‘yar shekara 14 fyade da aka bashi ita domin nema mata lafiya a jihar Adamawa.

Hukumar ‘yan sandan jihar ne suka bayyanawa manema labarai wannan labarin a ranar lahadi 23 ga watan Yuli, bayan sun kama mai maganin gargajiyar.

Mai maganin, Godwin Sanda ya kasance mazaunin kauyen Zagun dake karamar hukumar Numan a jihar ta Adamawa.

Kuma hukumar ‘yan sanda ta kama shi kan aikata lalatar daya yi da yarinyar, inda take cigaba da bincike akan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.