Hukumar ‘yan sandan Najeriya na jihar Adamawa ta damke wani matashi dake karbar kudade a hannun mutane da sunan cewa shi soja ne.
Matashi dan shekara 22 mai suna Paul Shaltha na karbar kudi ne a hannun masu tuka keke mai kafa uku, wato adaidaita sahu da kuma al’umma bakidaya.
Mai magana da yawun hukumar ‘yan sanda na jihar, Suleiman ne ya bayyana hakan yau ranar litinin.